Katin Gayyatar Daurin Auren Jaruma Halima Atete - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Katin Gayyatar Daurin Auren Jaruma Halima Atete

Nov 8, 2022
Masha Allah wannan abun yayi mana matukar sha’awa farin cikinmu shine Allah ya baiwa duk ya mace miji nagari tayi aure, 

a Masana’atar Kannywood kuma sai dauka ake daya bayan daya wannan tabbas duk cikarki ‘ya mace gidan miji yafi miki martaba da kima da daraja a nan duniya da lahira.AURE MARTABA
Fitacciyar Jarumar Finafinan Hausa Halima Yusuf Atete, tana dab da zama Amarya nan da kwanaki kalillan.

Za a daura auren Jarumar ne, da Angonta Mohammed Mohammed Kala, a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba 2022, da misalin karfe 10:30am na safe, a Abuja Sheraton Bus Stop, Juma’at Mosque, a garin Maiduguri, da ke Jihar Borno.

Kafin ranar daurin auren za a yi shagulgulan biki, da suka hada da Kwallon Kafa.