Ba zan iya sayar da “manpower” ko kayan mata a Saudiyya ba – Sadiyya Haruna - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Ba zan iya sayar da “manpower” ko kayan mata a Saudiyya ba – Sadiyya Haruna

Aug 30, 2023

Ba zan iya sayar da “manpower” ko kayan mata a Saudiyya ba – Sadiyya Haruna:Sadiyya Haruna ta ce ba za ta iya sayar da kayan da take sayarwa a Nijeriya a kasar Saudiyya ba.



A cikin gajeran bidiyo da ta wallafa, ta ce, ta gode da arzikin da Allah ya yi mata a Nijeriya; ba ta bukatar daukar maganin maza da kayan mata zuwa kasa mai tsarki.


Fitacciya a shafukan sada zumunta da aka jima ana zargin ta da batsa ta hanyar sayar da wadannan kayayyaki na shan cece-kuce a baya-bayan nan a kan tangardar da aurenta da mawaki G-Fresh ke fuskanta.


A wata hira da Sadiyya Haruna ta yi da DCL Hausa a 2021, ta ce, ba ta jin kunyar wadannan kayayyaki da take sayarwa.