-->
Yadda Tsohon saurayin budurwa ya harbe angon da zata aura ana tsaka da shagalin biki

Yadda Tsohon saurayin budurwa ya harbe angon da zata aura ana tsaka da shagalin bikiYadda Tsohon saurayin budurwa ya harbe angon da zata aura ana tsaka da shagalin biki:Kamar yadda Hausaloaded suka wallafa, Wani matashi ya je kutsa taron bikin budurwar da ta ki auren sa, ya harbi angonta a kan idon jama’a


Wani matashi ya kutsa taron daurin auren budurwar da ta ki auren sa, ya harbi angonta a gaban jama’a.


Al’ummar yankin Diyarbakır na kasar Turkiyya sun cika da mamakin aika-aikan matashin, inda ana tsaka da shagalin daurin auren, ya kutsa wurin ya bude wa angonta wuta, ya tsere.

Bidiyon da kafar yada labaran Yeni Şafak ta kasar Turkiyya ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna wani fusataccen matashi (sanye da farar riga da bakin wando) ya shiga dakin taron ya harbi ango (sanye da bakaken kaya), sannan ya fice a guje rike da bindigar.Aminiya na tattaro wannan labari.


Rahotanni sun nuna da farko wanda ake zargin ya yi wa amaryar tayin soyayyarsa, amma ta ki amincewa, shi kuma ya yi mata barazanar hallaka wanda za ta aura.To a ranar daurin aurenta ne ya shiga wurin taron bikin ya yi wa angonta wannan aika-aika, ya cika wandonsa da iska.


Angon ya samu rauni mai matukar hadari, sannan harsashin ya sami wani karamin yaro da ke kusa da shi a lokacin da aka yi harbin.


’Yan uwa da abokan arziki da sauran mahalarta taron bikin sun garzaya da su zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta dace.


Daga baya ne aka buda bidiyon bikin da kyamarar CCTV ta nada, aka gano wanda ya yi aika-aikan, aka shiga neman sa.Yan sandan kasar Turkiyya sun bi kwakkwafin bidiyon inda suka gano wanda ake zargin, suka shiga farautarsa, kafin daga daga karshe su yi nasarar cafke shi a maboyarsa.


Yanzu haka dai matashin yana amsa tambayoyi kafin a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel