Mun rasa mazajen aure shiyasa muka fara tallar kanmu a kafafen sadarwa - Yan matan Nijar - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Mun rasa mazajen aure shiyasa muka fara tallar kanmu a kafafen sadarwa - Yan matan Nijar

Dec 19, 2023


 Mun rasa mazajen aure shiyasa muka fara tallar kanmu a kafafen sadarwa - Yan matan Nijar

Kamar yadda Hausaloaded suka ruwaito cewa Wani sabon abu ya bullo kai a kasar jamhuriyyar nijar inda zankadiyar budurwa ko kwalamar bazawara sakin wawa suke talla kansu a kafafen sada zumunta koda za’a dace.


ATTENTION

For More Update Join Our WhatsApp Group 👇🏻

https://chat.whatsapp.com/GdEk2acGy4X8FFifk2wRtj

Follow Us On Google News 👇🏻

Naijastick On Google News 

Join Our Twitter Group 👇🏻

https://t.me/naijastickfansgroup

Wannan abun dai shine abinda yan matan kasar nijar sunka daura damara shine wakiliyar Dclhausa na samu zantawa da da wasu yan matan ga yadda hirar ta kasance tsakanin su.

“Sai da munka fara soyayya da shi na tura masa hotunana ya turomin nashi, sai na nunawa ƙawata tace wannan karya ne dan damfara ne ba auren ki zaiyi ba nima ya damfare ni’ inji rukayya daya daga cikin yan mata da suka tsalake rijiya da baya.

Tallata kai a kafafun sada zumunta ba sabon abu bane tsakanin budare da zawarawa, ita kam zainabu tace tana cigaba da tallata kanta a kafafun sada zumunta, saboda taga kawayenta sunyi kuma sun dace, ga abinda take cewa.

“Ina rubuta kalan jikina,ina rubuta shekaruna,ina rubuta kalan namiji da nake so dogo haka fari, in ma shekarunsa da kuma aikinsa, amma haryanzu bazan ce nayi dace ba, domin har yanzu ban samu kalan da nake so ba, amma ina saran zan samu saboda kawayena da dama sun samu ta wannan hanya – inji zainabu abu.

A halin yanzu rashin samun namijin aure ya zamo ruwan dare game duniya inda rashin samun hakan yasa wasu matan na shan tsangwama daga wajen mutane harda wasu kawayen su kamar yadda wata bazawara ta bayyana.

“Ko yanzu ciki ne nake baka ikon fita zuwa bukatan ka batare da an nuna karuwanci ka tafi ba, idan kazo gida sau goma baka da ikon wani motsi yanzu ana cewa baka son aure ka fison karuwanci , ni ke baiwa kaina aure ba Allah ke badawa ba”- inji wata bazawara da ta bayyana a boye sunan ta.

Amma duk da haka auren bazai wuce shekara guda ba’a samu rabuwa ba shin ko minene dalili ?

“Mata wata ran Ramatu hakuri ne basu da saboda koda yaushe sun fi son suna cikin daɗi, harka duniya yau taɓa kida taɓa karatu ce”- inji wani bawan Allah.

Ga hirar nan zaku iya saurare.

[Via