Amarya ta cakawa mijinta wuka da yake ƙokarin kwanciyar aure da ita, rai yayi halinsa - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Amarya ta cakawa mijinta wuka da yake ƙokarin kwanciyar aure da ita, rai yayi halinsa

Jan 1, 2024


Amarya ta cakawa mijinta wuka da yake ƙokarin kwanciyar aure da ita, rai yayi halinsa


Wata mata a jihar bauchi da ke arewancin nijeriya tayi sanadiyar mutuwar mijin ta da yake kokarin raya sunnah ta dalilin caka masa wuka da tayi dalilin haka rai yayi halinsa


Domin Shiga group namu don Jin labarai na Kannywood da sauransu ga link nan


>>> https://chat.whatsapp.com/Fmd72ZV4KczDfumgtH9Qs4


Wannan abun ya zamo ruwan dare ga mata a wannan ƙari ni musamman a matan hausawa idan kun tuna tun daga lokacin da maryam sanda ta kashe mijinta abun dai sai cigaba yake, inda kwanan ma wata hafsat chuchu ta kashe wani matashi a jihar kano.


Mun samu wani faifan bidiyo da yan jarida ke mata tambayoyi yayin da hukumar yan sanda tayi nasarar kamata.


Ga abinda take cewa:


“Anyi mana aure yazo zaiyi lalata da ni , shine naƙi yarda shine ya mamare ni ya dake ni shine na dauko wuka na daka masa a kirji inda na chaka wukar ma dan kadan ne shine ya fadi, a lokacin da ya fadi ba jini a jikinsa, sai anka garzaya asibiti anka ce rai yayi halinsa ya rasu”-inji amarya


Rundunar yan sanda ta jihar bauchi Dsp Ahmad Muhammad wakil PPRO na bauchi commad  yana cewa yarinya mai suna salma yar shekara sha takwas 18 anyi mata auren dangi ne, ita da dan uwanta, duka duka auren kwanan su goma sha daya, rundunar yan sanda ta  tambayi salma ko akwai dalilin da yasa ta kashe shi tace babu.


Amma a binciken yan sanda sun gano irin rikici da suke samu shi da ita na kokarin ya sadu da ita kamar yadda sunnah ta tana da shine ta caka masa wuka ya mutu.