Babbar Magana : Uwar adashe ta samu tabin hankali ranar kwasa - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Babbar Magana : Uwar adashe ta samu tabin hankali ranar kwasa

Jan 5, 2024


Babbar Magana : Uwar adashe ta samu tabin hankali ranar kwasa

Hankula sun tashi a garin Abba bayan ƙwaƙwalwar uwar adashe ta daina aiki ta rasa tunanin ta, ba za ta iya tunawa ko gane kowa ba,

Wata ‘yar Najeriya da ta shaida faruwar lamarin ta bayyana cewa, “mun shiga Uku, matar da aka damka wa alhakin tarawa da rike gudunmawar da mutane ke tarawa a Aba, jihar Abia, ta samu juyewar ƙwaƙwalwa”

Wakiliya ta ruwaito a cewar Daniel Eddy da ta wallafa a Facebook, “wannan mata, a halin yanzu ba ta iya gane kowa, da alama ta yi hasarar memory ta”

Rubutun Eddy ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, lamarin da ya haifar da martani daban-daban a inda da dama suka bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari mai ban tausayi.