Novel : Wayasan Gobe Hausa Novel 1 - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Novel : Wayasan Gobe Hausa Novel 1

Jan 1, 2024


Novel : Wayasan Gobe Hausa Novel 1


Barka da warhaka da fatan kuna Cikin koshin lafiya da kuma Kamala muna yi muku fatan hakan akoda Yaushe ...


Kamar yadda muka sani mun Saba da kawo muku labarai da kuma wasu daga Cikin recruitment kamar su Npower da dai sauransu.


Yau kam abin yasha babban da Wanda kuka Saba gani a wannan shafin namu Kai tsaye.. Zamu cigaba da kawo muku Novel akai akai domin nishadantarwa da kuma faranta ranku akoda Yaushe Ku kasance damu..


Domin Shiga group namu don Jin labarai na Kannywood da sauransu ga link nan


>>> https://chat.whatsapp.com/Fmd72ZV4KczDfumgtH9Qs4


Wayasan Gobe Hausa Novel 1


Umar ya tashina Cikin farin ciki da kuma walawala kamar yadda yasaba akoda Yaushe idan zaije makaranta, kamar dai kullum yauma yaje gaida mahaifiyarsa da kwana kuma ta amsa amsawa kamar yadda aka Saba harma takeyimai addua Wanda yake faranta ran Umar akoda Yaushe idan akace maka safiya ya waye.


Umar yaro ne Mai hankali da kuma Kamala ga kuma kyau ance son kowa kin Wanda ya Rasa a Hausa kenan, Umar ya kasance Yana karatu ne a wani college bayanda ya Gama makaranta secondary inda yayi karatun sa na primary school a wata qaramar makaranta anan Unguwar su dake Cikin garin jigawa dutse, Umar ba ruwanshi da Shiga abinda bai shafeshi ba Saidai Umar yabada wani abo Daya Wanda yazama masa halayya tun Yana qaraminsa wato tausayawa ga ko wanne halitta Hadi da Dan Adam da kuma dabbobi duk yabada tausayi akan wannan jinsin.


Bayan Rasa mahaifinshi a lokacin da ya kammala secondary school mahaifiyar Umar ya Zama itace wadda take daukar dawainiyar Umar na makaranta Shi wato makaranta college da yakeyi yanzu inda take Sanaa Wanda wannan sanaar ta Fara Shi ne tun kafin rasuwar mahaifin Umar shima dai Umar din baa barshi Baya ba domin yanada harkan da yakeyi duk da cewa yanzu dai karatu ne yasaka agaba.


Fitowar umar keda wuya ya kama hanyar Shi ta zuwa college tafiyar da yayi baiyi nisa da gida ba sosai Wanda yake aranar anyi ruwan Sama ne harma ruwan ya zuba sosai akan hanya inda mutane keta taka tsantsan akan wannan hanyar da ya kasance mutane suna yawan cinkoso a wannan hanyar domin zuwa Wajen harkokinsu na yau da kullum, ana haka sai Ga wata kyakkyawar budurwa sanye da tufafinta na makaranta Wanda ta saka farar hijabinne Wanda shine makaranta su yayarda dashi domin sanyawa, tana zuwa ta daidai hanyar da Umar shima yake zuwa, zuwan wannan budurwa keda wuya saiga wasu samari marar tausayi a cikin mota aguje kamar ba ruwa Sama akayiba kafin kace komai har sun zubar da wannan ruwan nan akan hijabin wannan yarinyar kuma suke wuce abinsu kamar ma Basu San meke faruwa.


Yarinyar takoma agefe tana tunanin yazata yi tunda hijabin ta ruwa ya batashi Ashe Umar Yana kallon duk abinda ya faru Wanda Shi ya kasance ne Yana gefen dayan titi itama tana gefen dayan kafin kace me Umar yatsallako ta gefen da Wannan kyakkyawar yarinyar take ..


Kome zai faru kuma muhadu akashi na biu 2 domin Jin yadda zata kasance.


Kasa Ku manta zaku iya share na wannan novel din zuwa Ga Yan uwa da abokai.