Takaitaccen tarihin Fidausi yahyaya ” Zainab Labarina” - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Takaitaccen tarihin Fidausi yahyaya ” Zainab Labarina”

Jan 24, 2024


Takaitaccen tarihin Fidausi yahyaya ” Zainab Labarina”


Kamar yadda shafin Hausaloaded suka rubuta Gidan jaridar BBC Hausa sun yi fira da jaruma Zainab al’amin ta cikin shirin labarina mai dogon zango amma asalin sunanta Nana Fidausi yahaya.

Nana Fidausi yahaya ta bayyana cewa ita har Sokoto ce amma asalin ta har nijar ce suna zama a sokoto ita ma iyayenta tayi furamari da sikandiri duk a Sokoto.


Nana Fidausi ta bayyana cewa irin yadda ta samu kanta a masana’atar Kannywood shine daman tun asalin ta son harka jaruma tun tana ƴar karama shine tayiwa wani dan uwanta da yake yana da kusan ci da yan kannywood din shine tayi masa magana yace to a sanya ta fim kai tsaye sai ta hannun Aminu saira ko Ali nuhu.

Shine anka samu malam Aminu saira yace zai sanya ni fim amma sai da yarda iyayena daga nan anka kira su, sunka aminta naje ankayi tirenin dina Shikenan na fara fim.


Nana Fidausi yahaya ta bayyana cewa malam Aminu saira shine ubangidan ta a masana’atar Kannywood, labarina shine fim dina na farko a kannywood amma yanzu haka akwai wanda ankayi ba’a fara haska shi ba.


Nana Fidausi yahaya ta bayyana cewa tana jindaɗi sosai ganin yadda masoyanta sunka damu da miyasa daga fitowar ta a fim har an kashe ta wannan nuna damuwar da sunkayi tayi farin ciki da shi sosai.

Bugu da kari nana Fidausi yahaya ta bayyanawa duniya cewa ita yanzu haka bata da saurayi.

Ga hirar ku kalla