Ali Nuhu kadai zan iya aure duk kannywood ta fadi dalili – Jaruma Radeeya Jibril


Ali Nuhu kadai zan iya aure duk kannywood ta fadi dalili – Jaruma Radeeya Jibril


A cikin shirin nishadi da gidan rediyo kanawa radio suna gabatarwa suna yiwa jaruma radeeya jibril kannywood tambaya wadda akan cewa.


Tambaya : fada muna mutum daya tak wanda zaki iya aure ba tare da ɓata lokacin ba kuma miye dalili?


“To gaskiya dole sai na amsa wannan tambaya a dan chanzamin wannan tambaya tunda kace akwai wasu tambayoyin amsata dan Allah nidai ka canza min wata


Jaruma Radeeya Jibril ta ce jarumi Ali Nuhu kadai zata iya tsamewa ta aure shi a fadin kannywood saboda yadda ya kware wajan kulawa da iyalinsa.”


Wata tambaya da anka yiwa jarumar itace.


Shin zaki iya komawa gidan tsohon mijinki ki cigaba da zama idan kuma baki iya komawa miye dalili.?


” Gaskiya a yanzu bazan  iya komawa gidan tsohon mijina  ba, domin ko na koma ba zata iya zaunawa ba.”


Mai tambaya: miye alakarki da Ty shaba?


“Ty shaba dai kawuna ne kamar yadda kowa ya sani, ina girmama shi ina daraja shi kuma akwai kauna saboda kauna ce ke saka wani abu, amma tace babu kalma i love You“.