Hoto na yafi wa Arewa muhimmanci akan yunwa da rashin tsaro -Hadiza Gabon
Shafin Hausaloaded sun ruwaito cewa Jarumar fina-finai Hadiza Gabon ta nuna mamakin ta kan yadda yan Najeriya musamman yan Arewa suka mance da matsalolin da ke addabar yankin suka maida hankali wajen tattaunawa da cece-kuce akan hoton ta,
Mahanga ta ruwaito wani Abubakar Sadiq Dankanjiba ne ya wallafa tambaya mai cike da mamaki cewa
“Yau kuma Topic din Hadiza Aliyu (Hadiza Gabon) ne (ke tashe) a TL din mutane arewa, ta yi kiba, tayi Rama toh Ina ruwanku Dan Allah.
Allah ya sawwaka dai..”
Cen sai ga Jarumar ta shiga muhawarar inda take martanin cewa ai kasan dayake hoton ne ya kawo masu garkuwa da mutane, ya kawo saɓo, ya kawo rashin tsaro da yunwa da tsadar rayuwa wanda ake fama da shi dole mutanen Arewa su maida hankali wajen cece-kucen akai.
Hadiza ta rubuta “Ai ta rame sai mun mayar da ita cikin mamanta, don tayi sabo ta kawo kidnapping/rashin tsaro/ yunwa da rashin sana’a dole ta zama topic a TL ..”
A makon nan ne dai hoton Jarumar ya karaɗe kafafen sadarwa a inda aka ganta ta saɓe ta rage ƙiba lamarin da ya jawo zafafan muhawara a shafukan sada zumunta ake ta muhawara akai, wasu na yabo wasu na kushewa cewa bata yi kyau a siririya ba gwara ta maido da ƙibar ta