Kotu taci tarar wata mata Naira ashirin ₦20 kan samun ta da laifin satar Naira Miliyan ukku 3M - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Kotu taci tarar wata mata Naira ashirin ₦20 kan samun ta da laifin satar Naira Miliyan ukku 3M

Feb 6, 2024


Kotu taci tarar wata mata Naira ashirin ₦20 kan samun ta da laifin satar Naira Miliyan ukku 3M


wani hukunci da za a dauka ga mari ga tsinka jaka, Alkalin babbar kotun Gombe, Mai shari’a Abdul Hamid ya bukaci wata da ake tuhuma, Rose Dogara Silas Gyar ta biya Naira 20 (Naira ashirin) ko ta fuskanci daurin shekara Uku a gidan yari bayan an same ta da laifin zambar Naira milyan Uku (N3 miliyan)


Mahanga ta ruwaito hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Gombe ce ta gurfanar da Gyar a gaban mai shari’a Hamid bisa zargin damfarar wani Saifullahi Sani Abdullahi na kudi Naira miliyan uku da sunan za ta taimaka masa wajen karbar rance a karkashin shirin noma na babban bankin Najeriya, CBN


Gyar da wani Mohammad Babayo Maina sun shaida wa Abdullahi cewa za su shigar da shi cikin shirin na CBN na Anchor Borrowers’ na manoma tare da alkawarin cewa zai samu kudade da tallafin noma daga bankin.


Gyar da abokinta sun yi nasarar karbar Naira miliyan Uku a hannun Abdullahi,


Sai dai Mahanga ta ruwaito Abdullahi ya kai su kara a EFCC a lokacin da bai samu komai daga CBN ba kuma sun ƙi maida masa kudinsa,


Mahanga ta ruwaito bayan an gurfanar da Gyar akan tuhumar da ake yi mata na zamba har N3,000,000.00 wanda abunda ta yi ya saɓawa sashe na 322 na kundin laifuffuka.


Ta amsa laifin da ake tuhumar ta da shi lokacin da aka karanta mata, wanda lauyan masu shigar da kara, M.D Aliyu ya roki kotu da ta yanke mata hukuncin da ya dace.


Sai dai lauyan wanda ake kara, Barrista S.O Kumu ya roki kotun da ta tausayawa matar, inda ya ce wanda yake karewa ta nuna nadama kuma ta mayar da cikakken kudin da ake zarginta da aikatawa.


PMNigeria ta ruwaito anan take mai shari’a Hamid ya yanke mata hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari ko kuma ta biya tarar N20 (Naira Ashirin).