Sautin Murya : Martanin mahaifiyar Murja kunya ƴar tiktok - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Sautin Murya : Martanin mahaifiyar Murja kunya ƴar tiktok

Feb 29, 2024


Sautin Murya : Martanin mahaifiyar Murja kunya ƴar tiktok


Bayan kamun da hukumar hisbah tayi wa fitacciyar yar Tiktok Murjanatu Ibrahim kunya wanda a kafar tiktok ke amfani da sunan yagamen yanzu dai tana asibitin dawanau inda take karkashin kulawar Hukumar hisbah har nan da wasu yan watani kafin a koma kotu.


Wani labari ya fito da ke nuna za’a yiwa murja kunya allurar mahaukata taƙi amincewa da ayi mata ita, shine fa mahaifiyar take mayar da magana akan wannan aika aikar da ake son yiwa diyar kamar yadda majiyarmu ta samu wani faifan sautin murya da dokin karfe tv na mahaiyarta ta bayyana.


Ga abinda take cewa


“Sunana haditul kubura, nice nan mahaifiyar Murjanatu Ibrahim kunya , ance an kaita asibiti ana mata magani naji na dauka na yarda, asibitin nasarawa, sai jiya wani abu ya taso anka kirani inyi maza maza inzo tana kuka da ranta za’a kashe min ita a takaice a guje naje asibitin dawanau na tarar da ita kuka, ni ina kuka munka rungumi juna.


“Ni kuma nace bana buƙatar ayiwa ƴarta allurar mahaukata don ba mahaukaciya bace, sai nake tambaya wannan ba asibitin mahaukata bace anka ce eh nace to miye dalilin kawo min ƴarta nan ayi mata allurar mahaukata.”


Baki ganin ko dan Abun da take akwai dan wani abu?

 


Sun tambaya nace ƴarta bata da komai , ƴarta lafiyar ta lau saboda daman tun tana kurciyarta haka ta taso da barkwancinta, kuma a haka take barkwancinta-inji mahaiyar murja kunya


Ga sautin murya da ankayi fira da ita nan.


Latsa nan domin saurare - (Via)