Ci-gaba a harkan kimiya: karon farko likitoci a Amurka sun dasawa mutum kodar alade - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Ci-gaba a harkan kimiya: karon farko likitoci a Amurka sun dasawa mutum kodar alade

Mar 23, 2024


Ci-gaba a harkan kimiya: karon farko likitoci a Amurka sun dasawa mutum kodar alade


Likitocin sun shafe tsawon sa’o’i 4 suna tiyatar dasa kodar bayan an jirkita kwayoyin halittarta, ga Richard Slayman mai shekaru 62, da ya jima yana fama da hawan jini da ciwon suga wato diabetes


Dw haus na ruwaito cewa, a karon farko likitoci a Amurka sun samu nasarar dashen kodar alade ga wani mara lafiya da ya sha faman jinyar ciwon koda da ke gargarar karshe a babban asibitin birnin Boston na jihar Massachusetts.

Kuma an taba yi masa dashen kodar a shekarar 2018, amma bayan shekaru 5 ta lalace har aka fara yi masa wankin koda.


Babban asibitin dai ya ce masu fama da ciwon koda sama da dubu daya da dari hudu ne ke jiran aikin dasa musu wata kodar bayan lalacewar ta su.


A baya can an taba yin aikin sanya kodar aladen ga wani mutum da kwakwalwarsa ta mutu, amma na yanzu shi ne aikin farko ga wanda yake raye. Haka zalika an taba dasawa wasu mutane biyu zuciyoyin aladen, amma daga bisani suka mutu kasa da watanni biyu da aikin.


~ Hausaloaded