Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Kama Mutum 11 Da Laifin Cin Abinci Lokacin Azumi
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama mutane 11 da suka hada da mata daya da maza goma saboda laifin cin abinci da rana tsaka a bainar jama’a cikin watan Ramadan a jihar.
An dai kama su ne yayin wani samame da dakarun hukumar suka kai unguwannin Sharada da Tudun Murtala dake Kananan Hukumomin Birni da kewaye da kuma Nassarawa a jihar.
Kakakin hukumar Hisbah, Lawal Fagge, ya bayyana cewa, sun kama maza goma da wata mace guda da aka samu ta na tallar gyada ta na kuma tafe tana ciye-ciye.
Ya bayyana cewa, hukumar ta gudanar da ayyukan bincikenta ne a duk fadin birnin, musamman ma kusa da kasuwanni.
Fagge, ya kuma bayyana cewa, wannan dokar ba ta shafi wadanda ba musulmai ba, amma idan sun sayar wa musulmi abinci a lokacin azumi, za a iya ganin hakan ya saba wa doka.
“Mun kama mutane 11 a ranar Talata, ciki har da wata yarinya da ke sayar da gyada. “Sauran 10 din maza ne, an yi kamen ne a fadin birnin musamman kusa da kasuwannin da ake tafka ta’asa.
“Ba mu kama wadanda ba musulmi ba saboda wannan bai shafe su ba, kuma kawai lokacin da za su iya yin wani laifi shi ne, idan muka gano suna dafa abinci don sayar wa musulmi da ya kamata su yi azumi.” Inji Fagge.
Musulmi su ne mafi rinjaye a al'ummar jihar Kano kuma jihar na bin tsarin shari'ar Musulunci sau da kafa wanda hakan ne ma ta sa aka kama mutanen.