MD Ali Nuhu ya tattauna da Netflix Akan Harkokin fina finai - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

MD Ali Nuhu ya tattauna da Netflix Akan Harkokin fina finai

Mar 11, 2024


MD Ali Nuhu ya tattauna da Netflix Akan Harkokin fina finai


Ali nuhu ya samu tattaunawa da Manhajar Netflix akan karfafa fina finai Nijeriya kamar yadda majiyarmu ta samu ta tsohuwar jaruma Wasila Ismail maƙasudin tattaunawa da kuma manufofin wannan taro tare da irin yadda anka samu mataya akan wannan taro.


Shugaban hukumar fina finai ta Najeriya Dr.Ali Nuhu Muhammad, yayi ganawa ta musamman da wasu daga cikin wakilan NETFLIX dake da babban ofishi a garin AMSTERDAM na kasar NETHERLAND.


An tattauna batutuwa akan yanda za’a bunkasa hukumomin shirye shiryen fina finai dake kudanci da arewacin Najeriya, NETFLIX sunci alwashin bada gudunmawa dari bisa dari dan ganin harkokin fina finai sun habaka ta bangarensu tare da jaddada goyon baya ga duk wani abu daya danganci sabon shugabancin hukumar ta fina finai ta Najeriya.


NETFLIX sunyi alkawarin bada dama ga duk kamfanonin dasuke kasar nan dan ganin cewa suma sun baje kolin hajarsu a kasuwanin fina finai na duniya baki dayan sa.


A karshe NETFLIX sun nuna farin cikin su kwarai dagaske game da matsayin da sabon MD Ali Nuhu ya samu, ganin cewa an ajiye kwarya a gurbinta, sun kuma gamsu cewa sabon shugaban zai bada cikakken hadin kan da zai kai hukumar zuwa ga mataki mai dorewa.