Yanzu Yanzu Alhaji Obobo Ya Sake Ɓaro Aiki, Ya Daura Niyya Zuwa Dubai A Keke


Yanzu Yanzu Alhaji Obobo Ya Sake Ɓaro Aiki, Ya Daura Niyya Zuwa Dubai A Keke 


Hazikin Matashin nan, kana gwarzo da ya je Makka a keke yanzu haka ya daura aniyar zuwa kasar Dubai kan keke a shekarar 2025 wato shekara mai zuwa.


Alhaji Ali Obobo wanda ya ki sayar da kekensa Naira miliyan 40 a Makka bayan da wani Balaraben kasar Egypt ya buƙaci a sayar masa da keken, amma yayi ƙememe saboda kishin Najeriya, ya kyautar da keken a gidan tarihi a Legas daga nan ne kuma yayi tattaki a kasa zuwa Maiduguri.


Yanzu haka ya daura niyar tattaki zuwa jihohi 6 bayan azumi, sannan kuma ya shaida wa AID Multimedia Hausa cewa a shekarar 2025 zai tafi Dubai a kan keke da yardar Allah.