Tsohuwar Matar Sani Danja Ta Yi Wani Sabon Aure, Mutane Sun Sanya Albarka
Rahotanni sun bayyana cewa tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta yi sabon aure shekaru uku bayan rabuwar ta da Sani Danja Aminiyar jarumar, Samira Ahmed ce ta tabbatar da hakan a shafinta na Instagram a daren ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024 Mutane da dama sun yi tsokaci kan wannan aure na Mansurah Isah wanda babu gayyata, inda wasu suka ce sun so ta koma gidan Danja
Rahoto da muka samu daga jarumar fina-finan Hausa, Samira Ahmed na nuni da cewa tsohuwar matar Sani Danja, Mansurah Isah ta yi sabon aure. An yi Auren Mansurah Isah ne makonni biyu bayan da tsofaffin ma'auratan suka aurar da 'yarsu, Riziqat Sani Danja.
Samira Ahmed, wadda aminiya ce ga Mansurah Isah ta ba da labarin sake auren tsohuwar jarumar a shafinta na Instagram.
Waiwaye:
Auren Sani Danja da Mansurah Isah An tafka soyayya ba 'yar kadan ba tsakanin Sani Danja da Mansurah Isah, tun suna fitowa a fim daya ake zargin jaruman na kaunar juna. Cikin ikon Allah, jaruman biyu suka amince da juna tare da zama ma'aurata, abin da ya kara masu daraja a masana'antar Kannywood. A shekarar 2018 ne Sani Danja da Mansurah Isah suka cika shekara 11 da yin aure, amma a shekarar 2021 lamura suka rincaɓe.
Auren Sani Danja da Mansurah Isah ya ƙare
A karshen watan Mayun 2021 ne Mansurah Isah ta shelanta wa duniya cewa aurenta da Sani Danja ya ƙare.
Mansurah Isah ta sha suka kan rabuwar ta da Sani Danja, inda har ta taɓa fitowa ta yi 'Allah ya isa' ga wadanda ke zaginta, tana mai cewa ba kanta farau ba.