Mahaifiyar jarumar Kannywood Feenah Adam ta riga mu gidan gaskiya
"Mahaifiya ta ita ce duniya ta.”
HAKA jarumar Kannywood Nafisa Adamou, wadda aka fi sani da Feenah Adam, ta rubuta a sitatus ɗin ta na WhatsApp a ranar 27 ga Disamba, 2022. Kusan shekara biyu bayan ta rubuta hakan, Feenah ba ta canja WhatsApp status ɗin nata ba, har zuwa yau ɗin nan.
Allahu Akbar! Mahaifiyar Nafisa, Hajiya Agaichata Kader, ta rasu a shekaranjiya Juma’a, 27 ga Satumba, 2024 da misalin ƙarfe 5:14 na asuba, bayan ta sha fama da rashin lafiya.
Dattijuwar mai kimanin shekara 60 ta rasu a wani asibiti mai suna Chi Lamorde Harobanda da ke birnin Yamai (Niamey).
An yi jana’izar ta bayan sallar Juma’a, daga nan aka kai ta gidan ta na gaskiya.
Marigayiyar ta rasu ta bar ‘ya’ya uku – mace ɗaya, maza biyu.
Da take labarta wa mujallar Fim batun wannan babban rashin, Feenah ta ce mahaifiyar tasu ta yi jinya ta tsawon mako biyu a asibiti, da ta samu sauƙi aka sallame ta.
Bayan kwana 17 da sallamar ta, sai kuma jikin ya ƙara tashi, aka mayar da ita asibiti.
“Kwana uku da mai da ta asibitin Allah ya ɗauki ran ta,” inji jarumar ‘yar ƙasar Nijar.
Ɗimbin ‘yan da sauran jama’a a Nijar, Nijeriya da sauran ƙasashe sun taya Feenah alhinin wannan babban rashi da ta yi, musamman bayan ta wallafa sanarwar rasuwar a soshiyal midiya.
‘Yan fim na Nijar da su ka je wa Feenah ta’aziyya sun haɗa da Baba Mitu, Rakiya Musa, Hamza Ɗan Filingué, Jafar Anzale, Barira Musa, A’isha, Aboulé, Mami Danke Danke, Binta Haske, Maryama Waziri, Sahabi Umar da Hamisu Gazawa.
Allah ya jiƙan Hajiya Agaichata Kader da rahama, kuma ya albarkaci abin da ta bari, amin.
Ɗimbin 'yan fim da sauran jama'a sun yi alhinin wannan babban rashi Allah yajikanta da rahamarsa Amin summa amin.