Mawaƙi Sunusi Anu zai aurar da ‘yar sa ta biyu


Mawaƙi Sunusi Anu zai aurar da ‘yar sa ta biyu


A RANAR Asabar, 4 ga Janairu, 2025, za a ɗaura auren ‘yar mawaƙi Sunusi Anu, wato Fadila Sunusi Anu (Anuwa), da angon ta Mubarak Usaini Zakariyya (Colorless).


Za a ɗaura auren ne a Masallacin Juma’a na Unguwar GRA, da ke Katsina da misalin ƙarfe 1 na rana.





Fadila dai ita ce ‘ya ta biyu da Alhaji Sunusi zai aurar bayan ya aurar da ‘yar sa ta farko, kuma ita ce ta uku a cikin ‘ya’yan sa.


Allah ya kai mu ranar lafiya.