Dalolin da Su Mr442 Suke Hoto dasu duk na Bogi Ne - Murja Yar Tiktok - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Dalolin da Su Mr442 Suke Hoto dasu duk na Bogi Ne - Murja Yar Tiktok

Nov 12, 2022
Murja Ibrahim Kunya ta Bayyana cewa Duk Dalolinda su Mawaki mr442 suke hoto dasu bana gaskiya bane na bogi ne domin naira dubu shida kawai tasan ta barosu da ita a alokacin da taje abuja wurin su.

Murja ita ta bayyana hakan a wata faifan vedio data wallafa a Shafin ta na TikTok inda tayi bayani Dalla dalla akan Dalolin da suke yawan Hotuna da vedio dasu a shafukan su na Tiktok.

Dukkan dai me bibiyar Shafin mawaki mr442 to zaiga cewa acikin makwanni biyun nan Zaiga suna yawan hotuna da daloli inda harma zakaga wasu lokutan suna kwanciya akansu.

Hakan yasa wani mabiyin Murja Ibrahim Kunya a kafar sadarwa na TikTok ya tambayeta akan dalolin dasu mr442 suke hotuna dasu shin na gaskiya ne? 

Gadai cikakken faifan bidiyon data wallafa nan a shafin nata.