Actress Hadiza Muhammad Exposed Her Final Ambition To Her Lovely Daughter - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Actress Hadiza Muhammad Exposed Her Final Ambition To Her Lovely Daughter

Jan 4, 2023


For More Hausa Update Please Join Our WhatsApp Group Now !!

Hadiza Muhammad was an famous female actress in kannywood film industry where she took a roll of many mother's in-law and such categories that made and lifted her career up to now.

The famous female actress Hadiza Muhammad was an Muslim she has a beautiful daughter who's celebrate celebrate her birthday party on the first day of the new year 2023 which is January 1.

She has exposed her final ambition to her daughter which you will see in the below caption of hausa version here.

Main tip's in Hausa now !!

Babban Burin Da Nake Da Shi a Kan Ƴata -Jaruma Hadiza Muhammad

Shahararriyar jarumar Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fi sani da Hadizan Saima, ta bayyana babban burin da take da shi game da ƴar ta Surayya Salisu Yahaya.

Jaruma Hadiza ta bayyana cewa babban burinta ga Surayya shine ta ga ta samu miji nagari domin raya sunnar Annabi Muhammad (SAW), inda tayi addu’ar Allah ya kawo miji nagari ga Surayya.

Hadiza ta yi wannan addu’ar ne a wata hira da Mujallar Fim kan bikin shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar Surayya da aka yi a birnin Kano.

An dai gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Janairu 2023.

“Lallai babu abin da zan ce da Allah sai godiya da ya nuna mani wannan rana domin wannan abin farin ciki ne a gare ni.”

“A yanzu babban burin da na ke fata shi ne Allah ya nuna mani lokacin auren ta. Ina fatan Allah ya ba ta miji nagari, kuma Allah ya ƙara mana shekaru masu albarka cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.” A cewar ta.

Ƴan fim da dama sun ɗora zafafan hotunan da Surayya tayi a shafukan su na sada zumunta domin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwar ta.