Hira Da Maryam Malika Inda Ta Bayyana Yadda Ayi Ta Dawo KannyWood Bayan Mutuwar Aurenta - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Hira Da Maryam Malika Inda Ta Bayyana Yadda Ayi Ta Dawo KannyWood Bayan Mutuwar Aurenta

Aug 6, 2023

Hira Da Maryam Malika Inda Ta Bayyana Yadda Ayi Ta Dawo KannyWood Bayan Mutuwar Aurenta.


Anyi Hirar Ne Tsakanin Hadiza Gabon Da Bakuwarta Wato Maryam Muhammad Malika, Wanda Yanzun Ake Kira Da Mero, Maryam Malika Ta Bayyanawa Duniya Wasu Zarge Zarge Da Akeyi Akanta Inda Ta Qaryata Su.


Da Farko Dai Mai Gabatarwa (Hadiza Gabon) Ta Fara Da Tambayar Maryam Malikan Kan Yadda Ya Taga Masana’antar KannyWood Inda Take Kafin Ta Tafi Tayi Aure Da Kuma Yanda Ta Dawo Ta Tarar Da Industry, Sai Bakuwar (Maryam Malika) Ta Bayyana Cewa An Sami Banbance Da Daman Gaske Musanman Ma Yanda Yanzun Ake Da Kayan Aiki Masu Kyau Fiye Dana Baya. Ta Kara Da Cewa Hatta Yadda Ake Tsarawa Ya Banbanta Da Na Baya,

Sai Hadiza Gabon Din Ta Tambayeta Shin Ya Yanayin Daukakarta Kafin Ta Tafi Tayi Aure Da Kuma Dawowarta.?


Sai Maryam Din Ta Bayyana Cewa Alhamdulillah! Har Yanzun Tana Da Masoya Kamar Yadda Ta Sami Masoya A Baya Kafin Tayi Aure.


Inda Tace Da A Baya Iya Manya Magidanta Ne Kawai Su Santa, Amma Yanzun Kuma Har Qananan Yara Ma Duk Sun Santa, Don Ko Fita Tayi Zataji Anata Kiran Sunanta.

An Tambayi Maryam Din Shin Ko Me Yayi Sanadiyyar Mutuwar Auren Nata, Kuma Shin Tana Son Mijin Nata Har Yanzun.


Bugu Da Kari Hadiza Gabon Din Kara Da Tambayar Maryam Din Wai Shin Dagaske Ne Abin Da Ake Cewa A Kotu A Raba Auren Nata Da Mijinta, Sai Maryam Din Taki Bada Amsa Tace Abar Wannan Maganar Kawai.


Mai Gabatarwa (Hadiza Gabon) Ta Tambaye Maryam Din Shin Menene GasKiyar Fada Da Tayi Da Producers Na Masana’antar KannyWood Kafin Tafiyar Auren Nata, Maryam Din Ta Bayyana Hakan A Matsayin Rashin Fahimta Na Mutane,


Inda Tace Koma An Sami Matsalar, Dama Zo Mu Zauna Ne Zo Mu Saba, Kuma Harshe Da Hakorina Ai Na Samun Matsala Wani Lokaci.


Nan Itama Maryam Malika Tayi Tambayarta Zuwa Ga Mai Gabatarwa, (Hadiza Gabon) Inta Take Tambayarta, Na Shigo Harkar Fim Na Tarar Dake Sannan Naje Nayi Aure Na Sake Dawowa Still Kinanan.

Sai Hadiza Gabon Din Ta Bayyana Cewa Aure Nufi Ne Na Allah, Sai Lokaci Yayi Mutum Zaiyi Shi.


Nan Ne Hirar Tasu Tazo Karshe.. Zamuci Gaba Da Kawo Muku Yadda Take Kasancewa A Gabon Talk Show Dama Wasu Bangarori Na Daban.