Samari sun fi son ƴar duma-duma shi ya sa nake shan sha-ka-fashe – inji wata budurwa - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Samari sun fi son ƴar duma-duma shi ya sa nake shan sha-ka-fashe – inji wata budurwa

Aug 13, 2023

Samari sun fi son ƴar duma-duma shi ya sa nake shan sha-ka-fashe – inji wata budurwa:Al’adar shan magunguna dai don kara ƙiba na ci gaba da zama ruwan dare a ƙasarnan musamman arewacinta duk da irin gargadi da likitoci ke yi kan illar hakan.jaridar dimokuraɗiyyar ce ta ruwaito wannan labarinToh amma duk da haka yan mata da matan aure sun dauki hakan tamkar wani ado ne don burge jama’a.


Wakilinmu a Bauchi Bashir Khalid Furyam ya tambayi wani ƙwararren likita game da illar hakan, inda ya tabbatar da cewa maganin na sha-ka-fashe na da matukar illa musamman yayin haihuwa.Dakta Hassan Garba wanda likita ne a asibitin Palycon dake cikin garin Bauchi ya tabbatar da cewa magungunar na sha -ka-fashe na haifar da cututtuka kamar su hawan Jini da cutar daji da ciwon Shuga da kuma ciwon zuciya sakamakon irin karfin sinadaran dake cikinsa.


“Wannan magani ya fi illa wa mata, saboda garkuwar jikinsu ba ta kai ta maza ƙwari ba, hakan ya sa da zarar sun yi amfani da magungunan sai ka ga ya fara tasiri a kansu”.


Toh sai dai duk da irin wadannan gargaɗi da likitoci irin su Dakta Hassan Garba ke yi, mata da dama na ci gaba da tsunduma gadan-gadan cikin wannan dabi’a kamar yadda wata matashiya a Bauchi ta shaida wa wakilin namu.


Matashiyar wacce ta buƙaci a sakaye sunanta, ta ce tana shan magungunar ƙara ƙiba ne sakamakon irin yadda samari ke nuna sha’awarsu ta son mace mai ƙiba da kuma irin yadda ake wa mata gori a guraben bukukuwa.


“Gaskiya dalilin da ya sa nake shan sha-ka-fashe shine irin yadda na ga yanzu kowa da kowa musamman samari, sun fi so su ga mace a cike kamar za ta tumbatsa, toh ni ma kuma ba na so a yi banda ni”


Toh sai dai duk da kasancewar matashiyar ta ce ba ta fara fuskantar wani kalubale ba sakamakon magungunar, amma ta ce tana fatan dainawa don gudun abinda zai kai ya komo.