Abin da ya sa muka yi bikin aurenmu irin na Indiyawa' - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Abin da ya sa muka yi bikin aurenmu irin na Indiyawa'

Jan 23, 2024

 

Abin da ya sa muka yi bikin aurenmu irin na Indiyawa'


Auren Dakta Mayana Sanusi Abubakar da Khadija Halliru na ɗaya daga cikin abubuwan da aka tattaunawa kansu a shafukan sada zumunta na arewacin Najeriya a makon da ya gabata.


Ma’auratan sun shirya wani biki wanda ba kasafai aka saba gani ba a yankin.


Amarya da ango sun caɓa ado da kaya irin na ƴan ƙasar Indiya, wani abu daya sa aka riƙa yaɗa bidiyo da hotunan bikin a shafukan sada zumunta.


Sai dai angon ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ya yi irin wannan auren ba, domina a aurensa na farko ma haka ya caɓa ado da kayan Indiyawa, shi da uwargidansa.


“Aurena na farko ma matata irin waɗannan kaya ta saka.”


Ya bayyana wa BBC Hausa cewa “Zama (a Indiya) ne ya sa al’adar Indiya ta shige ni kuma na ji ina sha’awar matata ta fito haka”.


Dakta Mayana ya bayyana wa BBC cewa ya kwashe shekara bakwai yana karatu a Indiya, inda daga wannan lokacin ne yake sha’awar al’audun al’ummar Indiya.


“Idan zama na sa mutum ya zama ɗan ƙasa (Indiya) to na zama, saboda shekara bakwai ba wasa ba ne,” in ji shi.


A nata ɓangaren, Khadija Halliru ta ce ta amince ta yi shigar Indiya a lokacin bikin auren shi ne saboda angon nata yana so.