ƴan bindiga sunyi awon-gaba da ango da amaryarsa a Zamfara - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

ƴan bindiga sunyi awon-gaba da ango da amaryarsa a Zamfara

Jan 30, 2024


ƴan bindiga sunyi awon-gaba da ango da amaryarsa a Zamfara


Yan bindiga a jihar Zamfara sun yi awon gaba da mutum hudu ciki harda ango da amaryarsa a harin da suka kai da tsakar dare a kauyen Madabanciya da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.


Wani mazaunin yankin ya shaidawa BBC cewa 'yan bindigar sun kwashe dabbobi da dukiyar jama’a da dama, tare da tilastawa mutanen kauyen kwana a cikin daji don tsoron sake kai masu hari.


"Irin sha biyu saura kwata na dare ‘yan fashi suka fado mana suka daukar mana mutum hudu, suka kwashi dukiya, akwai mata biyu da mata maza biyu, namiji guda da shi da matarsa aka dauke shi………ango da amarya ne."


Yan fashin dajin sun kuma sace kayan dakin amaryar da tufafinta kuma sun ci karensu babu babbaka saboda rashin jami'an tsaro a cewar mazaunin.


Yan bindigar sun afkawa garin saboda babu jami'an tsaro kusa da yankin da mayakan sa kai da za su rika sintirin.


"Wannan shi ne karon farko da 'yan fashin dajin suka shiga wannan yanki kuma a kasa suka shigo.


"Ban san inda suka ajiye abin hawarsu ba, kuma suna da yawa sosai rike da makamin nan da ake kira AK, suan ta harbata,"in ji ganau ɗin.


Mazaunin yankin ya yi ikirarin cewa 'yan sa kai da ke wani yankin da ke makwaftaka da su ne, su ka kai mu su dauki.


"Akwai wani yanki a kudancin Madabanciya da suke da ‘yan sa kai, da suka ji labari sun kawo dauki amma sun riga sun fita lokacin da suka taho."


Rundunar 'yan sanda ta jihar Zamfara ta ce ba ta da masaniya game da faruwar al'amarin.


ASP Yazid Abubakar wanda shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan ya shaida wa BBC cewa rashin samun bayyanai na cikin abubuwan da ke kawo mu su cikas a aikinsu. Shi yasa ba sa iya kai dauki a kan lokaci a cewarsa.


"Taimakon da muke so da ga wurin jama’a, in an samu bayyanai irin wannan a sanar da mu da wuri. Ba sai abu ya riga ya faru a ba mu labari ba."


Duk da cewa mahukuntan Najeriya na ci gaba da jaddada anniyarsu na kawo karshen matsalar ‘yan fashin daji a yankin arewa maso yammacin kasar, kawo yanzu mazauna wasu yankunan jihohi da matsalar ta yi kamari na ci gaba da fuskantar barazana daga wurin ‘yan fashin dajin.