Tagwayen da aka sace tun suna jarirai sun sake haduwa a Tik-tok - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Tagwayen da aka sace tun suna jarirai sun sake haduwa a Tik-tok

Jan 30, 2024


Tagwayen da aka sace tun suna jarirai sun sake haduwa a Tik-tok 


Amy da Ano tagwaye ne masu kama da juna, to sai dai jim kaɗan bayan haihuwarsu sai aka sace su daga wajen mahaifiyarsu aka kuma sayar da su ga iyalai daban-daban.


Tagwayen sun sun gano juna sakamakon ashirin wani gidan talbijin da ke nuna kyawawan bidiyoyin TikTok.


Yayin da suka shiga cikin abubuwan da suka faru a baya, sun fahimci cewa suna cikin dubban jarirai a Jojiya da aka sace daga asibitoci aka sayar, wasu a baya-bayan nan kamar a shekarar 2005. Yanzu suna sonin wasu amsoshi.


Amy na aiki ne a wani otal a birnin Leipzig. "Na tsorata kwarai da gaske''kamar yadda ta bayyana a firgice. ta ƙara da cewa ba ta yi barci ba tsawon mako guda.


Wannan ce damata ta ƙarshe ta samun wasu amsoshi game da abin da ya faru da mu."


'Yar'uwarta, Ano, na zaune a kan kujera, tana kallon bidiyon TikTok a cikin wayarta. "Na tabbata wannan ce matar da ta sayar da mu'', ta bayyana yayin da take zare idanu.


Ano ta yarda cewa tana cikin tashin hankali, amma ba ta san yadda za ta yi ba ko yadda za ta iya ɓoye ɓacin ranta.


An yi tafiya daga Jojiya a Amurka zuwa Jamus, da nufin gano tagwayen da suka ɓacewa juna, aɗanda a ƙarshe suka sake haɗuwa da mahaifyarsu.


Shekaru biyu da suka gabata sun yi ƙoƙarin adana abin da ya faru. Yayin da suke bayyana gaskiya, sun gano cewa suna cikin dubban jariran da aka ɗauke su daga asibitoci aka kuma sayar da su shekaru masu yawa da suka gabata.


Duk da yunkurin da hukumomi suka yi na gudanar da bincike kan abin da ya faru, har yanzu babu wanda aka tuhume shi da laifi.


Labarin yadda Amy da Ano suka gano juna ya fara tun suna da shekara 12.


Wata rana Amy Khvitia na zaune a gidan uwar ɗakinta a kusa da tekun Maliya, tana kallon wani shirin talabijin da ta fi so. Kwatsam sai ga wata yarinya tana rawa mai kama da ita. Ba ma kama kawai bar ta ba, a zahiri ta ga tamkar ita ce.