Labarin tausayi da muka sani kan Nabeeha da ƴan'uwanta da aka sace a Abuja - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Labarin tausayi da muka sani kan Nabeeha da ƴan'uwanta da aka sace a Abuja

Jan 17, 2024


Labarin tausayi da muka sani kan Nabeeha da ƴan'uwanta da aka sace a Abuja


Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar da cewa ta tura wata tawaga don ceto ƴan mata biyar da suka rage a hannun ƴan bindiga domin dawo da su gida.


A ranar Lahadi rundunar ta ce ta tura wata tawaga ta musamman don kubutar da ƴan matan iyalin Kadriya wadanda 'yan fashin daji suka sace a gidansu da ke yankin Bwari a Abuja.


Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa jami'an tsaro na kan lamarin.


“Rundunar na jagorantar wani hadin gwiwa a yunkurinta na magance abun da ya faru tare da kauce wa kara faruwar hakan. An hada karfi waje guda domin ceto wadanda aka sacen."


“Sai dai a bi abun da taka-tsantsan saboda yanayi ne mai sosa rai, don haka dole mu boye wasu bayanai saboda kada a janyo tsaiko a ayyukan da muke yi,” a cewar ƴansanda.


Inda ta kara da cewa yunƙurinta bai tsaya wajen ganowa tare da hukunta masu hannu a lamarin ba, rundunar ta ce za ta kara ƙaimi wajen ceto dukkanin mutanen da ake ci gaba da garkuwa da su.


A ranar Talata 2 ga watan Janairu, 2024 ne wasu ƴan fashin daji suka auka gidan su Nabeeha suka sace ta tare da mahaifinta da ƴan'uwanta mata biyar.


Bayanai sun nuna cewa daga bisani ƴan bindigar sun sako mahaifin, amma suka nemi a biya kuɗin fansa a kan ƴan matan shida.


Sai dai lamarin ya kai ga mutuwar Nabeeha, wadda ƴan bindigar suka kashe.


Batun sace ƴan matan da kisan Nabeeha, batu ne da ke ci gaba da jan hankali a kasar, musamman a dandalin sada zumunta, inda mutane ke ci gaba da bayyana fushinsu kan matsalar satar mutane da biyan kuɗin fansa.


Lamarin da ya jima yana ci wa al'umomi da dama musamman a arewacin ƙasar tuwo a ƙwarya, duk da yunƙurin da hukumomi suka ce suna yi na magance shi.


Matsalar da wasu ke ganin tana ƙara munana, musamman yanzu da take faruwa a birnin da fadar gwamnatin ƙasar da kusan dukkanin manyan ofisoshin tsaro na kasar suke.


Ita dai Nabeeha budurwa ce wadda ta kammala karatunta na digiri a harkar ilimin halittu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, sai kuma ƴar'uwarta Najeebah wadda ta karanci safiyo, wato 'Quantity Surveying' a jami'ar ta Ahmadu Bello.


Akwai kuma Nadheerah wadda ita kuma take a shekara ta uku a sashen harkar ajiye namun daji a jami'ar ta Ahmadu Bello.


Sauran ƴan'uwan nasu su ne Adeebah da Aneesah da kuma Mardiyyah.


Nabeeha da ƴar'uwarta waɗanda ke zama a garin Ilorin na jihar Kwara, sun je Abuja ne hutu.


Nabeeha ita ce ƴa ta biyu a cikin ƴaƴan mahaifinta wadda ake sa ran za a yi bikin yayenta a makarantar ranar 27 ga watan Janairu.


A ranar 2 ga watan Janairu ne ƴan bindiga suka auka gidan Alhaji Mansoor Al-Kadriyar da ke unguwar Bwari a Abuja, inda suka sace Alhaji Mansoor da ƴaƴan nasa shida.


Haka nan maharan sun kashe ƙaninsa Abdulfatah Al-Kadriyar tare da wasu ƴansanda waɗanda suka yi yunƙurin kuɓutar da yaran.