Matashi ya mayarda waya iPhone 13pro max bayan ya tsince wayar
A kwana kin baya an samu wani dan napep da ake jihar kano ya tsinci kudi sama da Naira miliyan goma sha biyar, ya mayarwa da mai abu kuɗi kayansa, hakan ya sanya ya samu kyaututtukan da dama sosai wanda har sarkin musulmi ya karamasa.
Haka zalika a jihar Yobe shima wani matashi dan keke napep ya tsinci naira miliyan 9 ya mayar shima ya samu karama da kyauta mai tsoka.
A yau din nan majiyarmu ta samu wani daga Muhammad kabir Aminu ya wallafa wani labarin matashi a shafinsa masha Allah shima yayi ƙokari sosai na tsintar wayar maƙudan kudi ya mayar.
Ga yadda labarin yake.
“Wannan Matashi Ɗan Katsina Ne Ya Tsinci Wayar Salula Ta Sama Da Milyan Guda Ya Kuma Maidama Mai Ita.
Kamar yadda mai bada labarin Vera Onyekwere tace Labani ya tsinci Wayar iPhone 13 Pro Max a cikin Keke Napep da yake tukawa bayan da ya ɗauki wannan Yarinyar da take cikin hoton nan ta mance wayar a Keken nashi.
Bayan ta kirawo wayar ta ya ɗauka ta buƙaci ya dawo mata da wayar ta yace tayi hakuri yana ɗauke da fasinja amma da zarar ya sauke su zai kawo Mata, haka akayi.
Lokacin da ya dawo ya kawo mata ta kasa gasgata ko mahwalki take ko a hwalke, ya bata wayar ta ya juya zai hau Keken shi ya kama gaban shi, shine ta kirawo shi tayi murna sosai ta ɗauki kuɗi ta bashi amma yace Bazai karɓa ba, sai da sukayi ta roƙon shi kafin ya amsa.
Anashi ɓangaren yace duk abinda ba nashi bane baya burge shi dan haka yasa da ta kirawo ya kawo mata wayar ta, domin Musulmi baya Sata ko ɗaukar abinda ba nashi bane.
Wannan yasa ta buƙaci tayi hoto dashi domin ta nuna godiyar ta, Labani dai kamar yadda ta bayyana Ɗan jihar Katsina ne.”