Abokan ango sun ƙarbo lefe daga gidan su amarya kwana Shidda kafin a daura aure
Kamar yadda shafin Hausaloaded suka rubuta. A cikin wannan yanayi da tsadar rayuwa da ake cikin Nijeriya da kuma rashin samun samarin aure wasu na nan kullum suna sallah dare da azumi Allah ya kawo musu mazan aure.
A lokacin wasu kuma sun samu amma akan rashin tawali da kwaɗayi sunga anyiwa kawayen su , dole suma sai anyi musu wannan wani labari ne da wani matashi ya bada a shafinsa na facebook Ahmed muntaqa yana cewa yarinyar da abokinsa ya nema saura kwanaki ladan za’a daura aure tayiwa kanta.
Ga yadda labarin yake.
“Cikin ikon Allah, yau na jagoranci tawagar abokanmu tsagin (No Nonsense) munje mun karɓo lefen abokinmu da ya kai bayan yarinyar tace ita lefen yayimata kaɗan. Jiya suna waya take fadamai lefen yayi kaɗan, abokanmu su hudu duk makanikai yau da asuba suka taho nan Abuja na wuce gaba mukaje muka karbo kayan lefen, mun bar yan gidan cikin rudani amma munce su tambayi yarsu koma meye. 10th February ne ranar auran. (Akwatu huɗu ne cike da kaya lefen).
Da ni dana jagoranci tawagar abokanmu, da shi abokin namu daya kai lefen (Dan-Ali) duk bamuyi nadamar karɓowa ba kuma mun wuce shafinta kenan har abada. Zamu nemarmai wata yar masu mutunci.
Yarinyar yan Kaduna ne, amma anan Maraba, Abuja suke zama. Abokinmu kuma dan Jos ne amma makanike ne a Abuja.”- inji Ahmed muntaqa.