Amarya Ta Yi Wa Mijinta Yankan Rago - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Amarya Ta Yi Wa Mijinta Yankan Rago

Feb 12, 2024


 Amarya Ta Yi Wa Mijinta Yankan Rago


Wata sabuwar amarya mai suna Aisha Aliyu da ke kauyen Nasarawa a Karamar Hukumar Lapai a Jihar Neja, ta yi wa angonta yankan rago.


Mazauna yankin sun tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin, inda suka ce amaryar ta hallaka angon ne da misalin karfe 1 na dare lokacin da mutane ke barci.


Rahotanni daga yankin sun ce ma’auratan sun yi aure ne a ranar 31 ga watan Disamban 2023.Wata majiya ta ce sabbin ma’auratan, sun samu matsala da yammacin ranar Lahadi.


Kazalika, majiyar ta ce an sulhunta ma’auratan kafin dare, amma cikin dare mahaifiyar angon ta ji shi yana kurma ihun neman dauki.


“Lokacin da mahaifiyarsa ta fito tare da wasu da ke zaune a gidan, sai suka samu angon kwance cikin jini. Angon ya yi kokarin tserewa daga dakin amma ya fadi a bakin kofa. Amma har yanzu ba mu san inda amaryar ta shiga ba.”


Majiyar ta ce amaryar ta fara daɓa wa angon wuka a kirji ne kafin daga bisani ta yi masa yankan rago.


Aminiya ta ruwaito cewa, Sabbin ma’auratan dai sun kwashe shekaru suna soyayya har zuwa lokacin da aka sa ranar bikinsu, amma daga baya amaryar ta sauya ra’ayinta.


“Amma duk da haka an warware matsalar. Sun fara soyayya tun suna makarantar sakandare. Amma kafin auren ta ce ba ta son ci gaba da soyayya da shi.


“Kuma an warware matsalar har ta yarda aka daura aure, ba tare da an san abin da ta shirya ba. Ta ce ta samu sabon saurayi,” a cewar majiyar.


Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin.


“Yau [Litinin] da misalin karfe 12:00 na dare muka samu rahoton wata mata mai suna Aisha Aliyu ta kashe mijinta, Idris Ahmadu da ke zaune a kauyen Nasarawa a Karamar Hukumar Lapai.


“Kafin zuwan jami’an ’yan sanda wadda ake zargin ta tsere, amma ana ci gaba da bincike don gano inda ta buya,” a cewarsa.


~ Hausaloaded