-->
Maganar Naziru Sarkin waka akan murna an canye nijeriya ya jawo cece kuce

Maganar Naziru Sarkin waka akan murna an canye nijeriya ya jawo cece kuce


Maganar Naziru Sarkin waka akan murna an canye nijeriya ya jawo cece kuce


Kamar yadda shafin Hausaloaded suka ruwaito cewa - Shahararren mawakin nan na nahiyar Afirka Naziru m ahmad wanda anka fi sani da sarkin waka yayi maganar nuna jin dadi da farin ciki kan rashin nasarar da nijeriya tayi a wasa kofin nahiyar Afirka afcon 2024 da ankayi a 11 ga watan Fabrairu na shekarar 2024 da anka buga a birnin abijan da ke kasar ivory coast, inda kasar ivory coast ce ta doke Nijeriya 1-2.


Sarkin waka ya wallafa wannan maganar ne jim kadan bayan tashi daga wasa da ankayi a daren lahadi a shafin na Instagram inda yake cewa.


“Ai duk wanda ma za su ji dadi, in an dauko kofin wanda suka ci, suka koshi ne fa, wanda bashi da abinci ko wanda yake hannun yan ta’adda ina yaga murna?.”


Wannan magana ta sanya mutane sunyi martani sosai a cikin rubutun inda suke Hausaloaded ta tattaro kadan daga cikin martanin mutane.


@ziter01 cewa yake yi:


Atoh , sai fada ake dani nan . Ban san ko zai rage tsadar rayuwa ko rashin tsaro ba. Ko zaisa dollar ta fadi. Just a distraction.


@sarkinwaka_san_kano yana mai cewa : @ziter001 ai duk wanda ma zasu ji dadi in an dauko kofin wannda suka ci suka koshine fa wanda bashi da abinci ko wanda yake hannun ya ta’adda ina yaga murna?


@m_mijinyawa_zainab cewa take yi :


ai basuga komai ba, wallahy adu’ar muce tasa basu ci african cup dinan ba..saboda munyi adu’a indai wannan cup din ba alkhairi ba ne Allah yasa kada aci shi. Gashi kuwa ba’a ci cup din ba.


@dandada_muhammad01 cewa yake yi:


Kishin kasa addini neh ! Duk wani ci gaba baya samuwa a kasa har Sai mutanen ckinta suna kishinta , for your information bh cup neh muke so bh kasarmu muke kishi da kauna.


@yahaya_ danjuma cewa yake: Be proud of your country at all costs, ira iranku ne sukayi yawa asama marasa kishin qasa, masu pretending suna qaunar qasassu, amma acikin zuciyarsu ba haka bane, da zuciya ake nuna kishi ba da baki bah, yakamata kasan cewa kai babba ne acikin al’umma, kasan kalan maganganun daza ka rinqa padi a Media. @sarkin_wakar_san_kano

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel