Kashi tamanin 80% mata da ke fim, ba da son iyayen su ba – Adam a zango - Naija Stick

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Kashi tamanin 80% mata da ke fim, ba da son iyayen su ba – Adam a zango

Feb 17, 2024


Kashi tamanin 80% mata da ke fim, ba da son iyayen su ba – Adam a zango


Fitaccen Jarumi kuka mawaki Adam a zango a wata fira da yayi da jaridar BBC Hausa a shirin mahangar zamani ya bayyana cewa mafi yawan yan matan kannywood da suke harka fim sunfi karfin iyayen su domin ba da son su Shigo harka fim ba.


Ga abinda yake cewa.


“Abinda nake so mutane su fahimta shine duk namiji ko macen da aka ce ta tsallake gidan su ta shigo harka fim, ina so kowa ya tabbatar da cewa bada son iyayenta bane.


Wata kila tafi karfin su ne , ta shigo dole ne basa so ko kuma basu da sha’awa yar su tayi fim amma tana so zasu barta, duk wadda iyayenta sunka kasa cewa ta zauna a gida , tace bazata zauna ba , ta fito tayi fim waye cikin yan fim ya isa yace ta koma gida ki zauna babu shi.


Indai tana da wa, da kane, uwa, uba kawu suka kasa hana ta shigowa kannywood, miyasa duniya kullum take tunanin mune zamu tarbiyyan tar da su?


Bayan sun baro iyayen su kashi tamanin 80% wadanda suka shigo masana’atar mata dan su maza iyayen su ba sai sun zaɓa musu sana’ar da zasu yi ba, basu da wannan matsala, amma mata iyayen 80% basa so suka shigo .


Wata ma sai ta fara fim din iyayenta su zo su dauke ta su tafi da ita, wata ma matar aure ce , to kin bar iyayen ki, kin bar mijinki kin shigo fim , waye cikin yan fim ya isa yace karki tashi, karki zauna, kwanta kiyi bacci, kar kije wuri kaza, karki barki abu kaza babu wanda ya isa.


Dan haka muna yin iya yin mu ne muga cewa abinda Mace zata iya aikatawa cikin masana’atar mai girma bai shafi harka mu ba, kuma na yarda da karbe ki badan na isa in baki tarbiyya ba, a’a sai dan kin shigo cikin sana’a ta, kina da yanayin zaki iya zama jaruma in baki gudunmuwa ta daidai gwargwado iyawa ta , in baki tarbiyya dai-dai gwargwado iyawa ta, amma daga nan babu wani abu da zan iya yimiki da wuce Ke da kanki ki kula da rayuwarki – inji adam a zango”