Na Rantse da Allah Ina matukar son Nafisa Abdullahi – Abu Sarki - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Na Rantse da Allah Ina matukar son Nafisa Abdullahi – Abu Sarki

Feb 17, 2024


Na Rantse da Allah Ina matukar son Nafisa Abdullahi – Abu Sarki


Sunana Abu Sarki haifaffen garin Zaria dake jihar Kaduna. Ina da shekara 29 mazauni jihar Kano, ku taya ni isar da sakon dan Allah.


Sako ne kai tsaye nake son isarwa daga zuciyata na kamu da so da kaunar wannan baiwar Allah Nafisat Abdullahi wadda fitacciyar jarumar finanfinan Hausa ce wacca tauraruwarta take haskawa.


Na sani cewar ba za a taba had’a hanyar jirgi da mota ba amma ita zuciya babu ruwanta da hangen matsayi ko mukami kamar yadda zuciyata ba ta taba kallon Nafisat Abdullahi a matsayin da take ba illa iyaka dai na san ina sonta, ina kaunarta saboda Allah.


Nafisat mace ce da duk namiji za iyi mafarkin samun ta a rayuwarsa, a kowacce soyayyya akwai labarin bakin ciki, a kowanne labarin bakin ciki karshensa nasara saboda haka ba zan taba fidda rai da abun da nake so ba duba da matsayin da kike da matsayin da nake a yanzu.


Na kara kasuwa sosai wallahi zuciyata tana sonki amma zuciyata ita ba ta da tantance matsayi ko daukaka kawai kamuwa take na yarda da hakan.


Dan Allah ki amincemin na ganki ko zan samu nutsuwa a cikin zuciyata wallahi so da kauna abu ne mai girman gaske.


Amma idan baki amince min ba zuciyata za ta iya samun damuwa domin na san nayi babban rashi na rashin ganin ki a zahiri da ba na yi, haka kuma zan karbi wannan bakin cikin a cikin shafukan rayuwata. Fata na dai ki yi rayuwar farin ciki a duk inda kike.