Tsananin Rayuwa: Dan Agaji ya tsinci kuɗi kimanin naira miliyan 100 ya baiwa mai abu, kayansa


Tsananin Rayuwa: Dan Agaji ya tsinci kuɗi kimanin naira miliyan 100 ya baiwa mai abu, kayansa


Allahu Akbar duk tsananin yunwa da talauci da rayuwa da ake ciki na Allah basa ƙarewa a koda yaushe inda anka samu wani matashin saurayi mai rayuwar sahabbai yayi wani abun a yaba inda ya tsinci zunzurutun kudi masu yawa amma ya mayar da su kamar yadda wani bawan Allah ya bada labarin faruwar abun Adamu Ali assunnah ya wallafa a shafinsa yana cewa.


Cikin ƙaddarawan Allah, wannan Yaro ya tsinci wata Jaka da take shaƙe da maƙudan kuɗi a Katsina da aka ƙiyasta kuɗin sun kai 100 million


Kuɗaɗe ne na ƙasa huɗu a haɗe wuri guda.


Bayan ya tsinci kuɗin, yayi shigiya kuma an sami mai kuɗin wata mata ce ƴar Kano


Salihu Abdul-Hadi Ɗan Agaji ya nuna kyakkyawar tarbiyyar da aka bashi a gidansu da kuma wanda rundunar Agaji ta bashi, ya mayar da kuɗi zuwa ga mai su.


Bayan ta buɗe jaka taga kuɗi yadda suke ba’a taɓa komai ba, ta dubi Salihu tace amma kai ba mutum ba ne don mamaki a wannan hali da ake ciki mutum ya tsinci irin wannan kuɗi kuma ya dawo dasu.


Ba wannan ne abin sha’awan ba


Matan nan ta ɗauki kuɗi a cikin wannan kuɗin cikin farin ciki, ta baiwa yaron nan, amma mahaifiyar sa ta hana shi karɓa


Sakamakon haka, a yau Shugaba Ash-sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya karrama shi ya bashi lambar yabo tare da haɗa masa da kujerar Makkah.

Gwamnan Bauchi ya bashi Mota Bus domin ya kama sana’a.


Ɗan majalisar tarayya daga Jihar Zamfara ya bashi naira miliyan biyu 2.


Muna roƙon Allah ya azurtamu da irin wannan amanar mu da dukkan iyalanmu.

Previous Post Next Post