Yanzu- Yanzu : Sheikh Daurawa ya dawo mukaminsa na Hisbah


Yanzu- Yanzu : Sheikh Daurawa ya dawo mukaminsa na Hisbah


Bayan wata ganawa da akayi tsakanin gwamnan Kano da kuma zauren hadin kan malaman jihar karshe an cimma matsayar sheik Aminu Ibrahim Daurawa zai koma kujerar sa ta shugabancin hukumar Hisba.


Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa yace bayan dogon nazari kungiyar ta fahimci shedan ne ya so shiga tsakanin gwamnan Kano da sheik Malam Aminu Daurawa.


A baya bayan nan ne dai gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf yayi wasu kalamai dake nuna rashin gamsuwa da ayyukan hukumar Hisba wanda kalaman ya sabbaba saukar Malam Daurawa daga mukamin sa.


A daren wannan Litinin dai zauren hadin kan malaman suka yi wannan zama da gwamnan Kano, inda a karshe aka cimma matsayar sulhu kuma nan take Malam Aminu Daurawa ya amince zai cigaba da jagorantar hukumar ta Hisba