Magidanci Da Zai Ƙara Aure Ya Yabi Uwargidansa Lokacin Da Yake Jimamin Yi Mata Kishiya


Magidanci Da Zai Ƙara Aure Ya Yabi Uwargidansa Lokacin Da Yake Jimamin Yi Mata Kishiya 


Hassan Muhammad Al Hassan da ke Zaune A Kudancin Najeriya ɗaya ne daga cikin masu bibiyar AID Multimedia Hausa kuma aminin wannan kafa ta sadarwa ne, wanda ake shirin bikin ɗaurin Aurensa na biyu a jihar Kano bayan Sallah Babba cikin yardar Allah, a shafinsa na soshiyal Midiya ya shaida cewa zai kara aure ne ba don gazawar Uwargidansa ba, domin yana son ta fiye da ƙima, sai don ƙaddara kawai zai ƙara auren,  kasancewar ta ciri tuta, tayi masa kami da komai.Hassan Muhammad Al Hassan Ya ce, "Zan yi ƙarin aure amma kusani ina son matana fiye da’kima.


 "Dalilin wannan post ina so na fashimtar da wasu tsirarun mutane wallahi Maman Abdull ta dabance ina sonta matu’ƙa, bisa waɗannan dalilai da na kawo a ƙasa  

(1) Mace ce mai yawan  addini 

(2)Mace ce mai yawan haƙuri da juriya 

(3)Mace ce mai yawan ri’kon amana 

(4)Mace yawan gaskiya 

(5)Mace mai yawan yawan biyayya 

(6)Mace mai  girma mabagatana da ‘yan uwana

(7) Mace mara  kwaɗayi 

(8)Duniya wallahi  bata dame taba

(9) Mace ce mai yawan tsoron Allah 

(10) Macece mai yawan tausayi "Wani lokacin Nakan tambayan kaina Wai shin mene dalilina na son ƙara aure? 


"Amsa, ƙaddara kawai…… ina sonki uwar ‘ya'yana,  Maman Abdull da Bilal da Ma’eesha


Cewar Hassan Muhammad Al Hassan"

Previous Post Next Post