Sarki Sanusi Da Sarki Aminu Zasu Jagoranci Sallar Juma'a A Kano
A lokacin da ake ci gaba da dambawar sarauta a birnin Kano, zuwa yanzu Kwamishinan 'yan sandan Kano CP Usaini Gumel ya shaida cewa Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido ne zai jagoranci sallar juma'a a masallacin juma'a na cikin garin Kano da ke gidan Sarkin Kano na
Muhammadu Rumfa, yayin da Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero zai jagoranci sallar juma'a a masallacin da ke gidan Sarki na Nasarawa.
Me kuka fahimta da wannan?
Ta tabbata sarki biyu ne a Kano?