YANZU - YANZU: Matashin Malami mai da’awah, Mufti Yaks ya rasú


Allah Ya yi wa matashin malamin nan Abdullateef Aliyu Maitaki, wanda aka fi sani da Mufti Yaks rásúwâ.


Sheikh Isa Ali Pantami ne ya wallafa labarin rasúwar ta matashin malamin, wanda ya ke kwaikwayòn shararren malamin nan Mufti Menk, a shafinsa na Facèbook a yau Asabar da safe.Pantami, wanda ya baiyana kaɗuwar sa da rasúwar matashin malamin, wañda ya ke gabatar da wa’azuzzukañ sa da turanci ta kafafen sada zumunta, ya ce za a yi jana’izar sa da ƙarfe 10 na safe a layin Justice Maiyaki, Dutsén Kura Gwari, Minna, Jihar Neja.Marigayi Mufty Yaks sananne ne wajén da’awah (kira zuwa ga Musúlunci) a ciki da wajén Nájeriya.


Mu na fatan Allah Ya karbi dukkanin aiyukansa na alkhairi, Ya sa aljannar Firdaus ta zama makòmarsa, Ameen.

Previous Post Next Post