An yi taron addu’ar cika shekara 1 da rasuwar Darakta Aminu S Bono - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

An yi taron addu’ar cika shekara 1 da rasuwar Darakta Aminu S Bono

Nov 17, 2024


An yi taron addu’ar cika shekara 1 da rasuwar Darakta Aminu S Bono


Cikin ƙudirar Allah da ikon sa, marigayi Darakta kuma Jarumi, Aminu S Bono, ya cika shekara ɗaya da komawar sa ga Allah.



Domin kuwa a rana irin ta yau 17 ga Nuwamba 2023 Allah ya yi masa rasuwa.


Shekara guda dai kamar kwana guda ce ga duk wanda Allah ya yi wa tsawon rai.


Hakan ta sa tsawon shekarar ‘yan uwa da abokan arziƙi a kullum suke tuna shi.


Don haka, a safiyar wannan rana ta lahadi 17 ga Nuwamba 2024 wasu daga cikin aminai da ‘yan uwa suka shirya taron addu’ar cika shekara guda da rasuwar sa.



Taron addu’ar dai an shirya shi ne a ƙofar gidan su marigayin dake Unguwar Dandago a cikin birnin Kano.


Kamar yadda ɗan uwa kuma babban abokin Darakta Aminu S Bono, Malam Misbahu M Fada, ya shaida mana, sun shirya taron ne domin tunawa da shi da kuma yi masa addu’ar nema masa gafara a wajen Allah tare da dukkan musulmi da suka riga mu gidan gaskiya, da mu ma idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da imani.


An dai yi taron addu’ar an gama lafiya. Da fatan Allah ya ji ƙan Darakta Aminu S Bono.