An ɗaura auren Jarumin Barkwanci Ayatullahi Tage
Da safiyar ranar Lahadi, 17 ga Nuwamba, 2024 ne aka ɗaura auren Jarumin Barkwanci Ayatullahi Tage tare da amaryar sa Hauwa Muhammad Isah (Hauwa Madu).
Auren da aka ɗaura da misalin ƙarfe 11 a Unguwar Tudun Murtala Kwanar Tifa ya samu halartar jama’a da dama da suka zo domin shaida auren.
Cikin ‘yan fim ɗin da suka samu halartar wajen taron ɗaurin auren har da fitaccen Jarumi Nuhu Abdullahi.
Da fatan Allah ya bada zaman lafiya da albarka a cikin zaman auren.