An Bude Shafin Cike Shirin Rice Master Training Programme (RMTP) 2025
Ina Manoman Shinkafa, An Bude Shafin Cike Shirin Rice Master Training Programme (RMTP) 2025
Shirin Rice Master Training Programme (RMTP) na farko zai gudana daga 27 ga Janairu zuwa 1 ga Fabrairu, 2025 a Ghana. Wannan horon mai tsawon watanni 7, wanda zai kasance a cikin rukunai uku, an tsara shi domin inganta fasaha da dabaru a cikin tsarin samar da shinkafa. Ana gayyatar kwararru a bangaren shinkafa su nemi wannan dama mai muhimmanci.
Shirin zai mayar da hankali kan fannoni kamar samar da shinkafa mai dorewa, kulawa bayan girbi, sarrafawa da ƙara darajar shinkafa, da kuma inganta haɗin kai tsakanin jinsi. Za a kuma horar da masu halarta kan dabarun shugabanci da sadarwa.
Duk kuɗaɗen masauki, abinci, da sufuri za a ɗau nauyi. Ana buƙatar masu sha’awa su cike fom ɗin
Domin cike form ga link akasa:
kafin 8 ga Disamba, 2024. Domin ƙarin bayani, a tuntuɓi: C.Kacou@cgiar.org ko joseph.atakora@giz.de. Wannan dama ce ta musamman ga ƙwararrun tsarin shinkafa.
Ziyarci shafin su anan:
Visit Web link here