Hukumar Tace Finafinai ta maka Mawaki Rarara a kotu
HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta gurfanar da mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) a gaban Kotun Majistare mai lamba 47 da ke Nomaslad bisa zargin sa da sakin wata sabuwar waƙa ba tare da sahalewar hukumar ba.
A wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya aika ga manema labarai, ya ce, “Tun kafin wannan lokaci Hukumar Tace Finafinai ta aika wa mawaƙi Dauda Kahutu Rarara saƙon ƙorafi dangane da sabuwar waƙar da ya saki ba tare da ya kawo an tace ba. Sai dai mawaƙin bai ba ta amsa dangane da ƙorafin da ta aika masa ba, wanda hakan ne dalilin da ya sa hukumar ta maka shi a kotun domin kowa yana zaman doka ne.”
Wakilin hukumar a kotu ya tabbatar da cewa tuni kotun ta aika wa da mawaƙin takardar gayyata, sai dai kuma a zaman kotun na yau Laraba, 13 ga Nuwamba, Rarara ko lauyan sa ba su je kotun ba a yayin zaman ta kan kes ɗin.
Tun bayan sakin sabuwar waƙar, Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta tura wa mawaƙin saƙon neman ba’asi ta hanyar saƙon kar-ta-kwana, amma bai ba da amsa ba.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa tace waƙa yana ɗaya daga cikin ayyukan hukumar domin tabbatar da tsafta tare da ɗora komai a bisa doron doka da oda.