Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

Nov 16, 2024


Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah


Tsohuwar jaruma kuma furodusa a Kannywood, Hajiya Mansurah Isah, ta samo wani babban tallafi daga Cibiyar Haɓaka Fasahar Yaɗa Labarai ta Ƙasa, wato National Information Technology Development Agency (NITDA), wanda take da burin yin amfani da shi wajen taimaka wa matan Kannywood domin su dogara da kan su. 

Ta ce ya dace da su a maimakon su riƙa fitowa a matsayin jarumai kawai, wanda daga an daina yayin su ko suka yi aure, shi kenan sana’ar tasu ta tsaya. 

A ganin ta, wannan tallafi wata dama ce ta samu da za ta koyar da matan duk wasu harkoki na sana’ar fim don a kawar masu da tunanin cewar sai aktin kawai za su iya.


A Turance, kayayyakin da NITDA ta ba Mansurah su ne:


  1. Alienware M18 R2 gaming laptop
  2. TraceMR178i gaming desktop
  3. 4K monitors
  4. Maverick 1550VA UPS
  5. Adobe Premiere 2024 software
  6. Internal and external SSD drives
  7. 40-inch smart TV
  8. DaVinci Resolve Studio
  9. Plural Eyes software 
  10. Cinema line camera
  11. high-quality lenses
  12. Memory cards
  13. 1 professional tripod a mini drone


Haka kuma ta bayyana burin da take da shi don ganin masana’antar Kannywood ta ci moriyar wannan tallafin.


FIM: Mansurah Isah, mun samu labarin wani tallafin kayayyakin bunƙasa harkar fim da kika samu daga Gwamnatin Tarayya ta ƙarƙashin National Information Technology Development Agency (NITDA). Ya aka yi kika samu wannan tallafin da kuma yadda za ku yi amfani da shi don bunƙasa harkar fim?


MANSURAH ISAH: To, da farko bayan sallama zan gabatar da kai na a matsayin jaruma, furodusa, darakta, kuma a matsayi na na mace a cikin Kannywood duba da yadda maza ne suke da ƙarfi a kowane ɓangare na harkar, zan iya cewa ma sun mamaye komai, saboda furodusa ɗin za ka ga duk maza ne, darakta da sauran ɓangarori za ka ga duk maza ne.

A tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, Hajiya Mansurah ta bayyana yadda ta samu wannan tallafin daga Gwamnatin Tarayya da kuma hanyoyin da ta bi don ganin an cimma nasarar samun sa.