Jarumar Kannywood, Fati Ladan da Yerima Shettima sun samu ƙaruwa a karo na uku - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Jarumar Kannywood, Fati Ladan da Yerima Shettima sun samu ƙaruwa a karo na uku

Nov 7, 2024


Jarumar Kannywood, Fati Ladan da Yerima Shettima sun samu ƙaruwa a karo na uku


DA safiyar ranar Talata, 4 ga Nuwamba, 2024 Allah ya azurta tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Fati Ladan da santaleliyar ‘ya mace.


Fati ta haihu da misalin ƙarfe 10:00 na safe a asibitin Barikin Sojojin Sama (Air Force Base) da ke Mando, Kaduna.


Kamar yadda mijin ta ya shaida wa mujallar Fim, ya ce, “Hajiya Fati da jaririyar su na cikin ƙoshin lafiya.”


Wannan ita ce haihuwar Fati ta huɗu. Na farko ta haifi ɗa namiji, wanda kafin a yi suna Allah ya ɗauki abin sa, sai kuma a shekarar 2019 ta haifi Humaira, a 2022 kuma ta haifi Ameer.


Fati Ladan dai ta na auren fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa na Matasan Nijeriya (Arewa Youth Consultative Forum), Alhaji Yerima Shettima.


Allah ya raya ta, ya kuma albarkaci rayuwar ta.