Ni ba ɗan daba ba ne, inji Garzali na shirin ‘Daɗin Kowa’ - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Ni ba ɗan daba ba ne, inji Garzali na shirin ‘Daɗin Kowa’

Nov 8, 2024


Ni ba ɗan daba ba ne, inji Garzali na shirin ‘Daɗin Kowa’


Jarumi Amir Iliyasu Maiross, wanda aka fi sani da Garzali a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, ya bayyana cewa shi fa ba ɗan daba ba ne.


A cewar sa, yanayin da yake fitowa a fim ne ya sa wasu suke yi masa kallon ɗan daba, amma shi rayuwar sa ta zahiri ba ɗan daba ba ne kuma bai taɓa yin harkar daba ba.


A lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim a game da kallon da ake yi masa na ɗan daba, Maiross ya ce: “Yanayi ne ya sa ake kallo na kamar ɗan daba, saboda a yanzu ina fitowa a matsayin Garzali a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, amma tsawon lokacin da na yi ina fitowa a cikin finafinai ai ba a yi mini irin wannan kallon.


“Na shafe sama da shekaru ashirin ina harkar fim a matsayin jarumi, darakta kuma furodusa, domin ka ga ni na shirya fim ɗin ‘Jarin Ibro’ kuma a nan na samu sunan Amir Maiross, kuma ni na shirya ‘Asusun Ibro’ da sauran finafinai tun a wancan lokacin.


“To kuma a yanzu sai Allah ya kawo mini wata ɗaukakar da sunan Garzali, ko Gazza a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’. Ina alfahari da wannan dama da na samu kuma ina godiya ga Allah.”


Ya ci gaba da cewa: “Wannan rol ɗin ya sa na samu ɗimbin masoya a ciki da wajen ƙasar nan da nake alfahari da su. Don ba zan manta ba an ɗauki tawagar ‘yan fim na je ƙasar Nijar don mu gabatar da wasa, sai na tsaya a matsayin mai tsaron ƙofa, amma maimakon mutane idan sun zo su shiga, sai kawai su tsaya kallo na, wanda daga ƙarshe sai ɓoye ni aka yi saboda jama’a sun yi mini yawa.”


Ya ƙara da cewa, “A wannan rol ɗin da nake fitowa ya sa har Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, sun shirya taro sun kira ni a matsayin wanda na yi faɗakarwa a kan illar shaye-shaye da kuma harkar daba.


“Sannan kuma idan na haɗu da masu shaye-shaye da ‘yan daba sai su ɗauka nasu ne mu yi wasa da dariya har ma na yi musu nasiha a kan harkar daba da kuma illar ta .


"Sannan ina samun alheri da kuma alfarma a duk inda na je saboda wannan suna na Garzali.


“To ina godiya da ɗaukakar da na samu. Kuma ina kira ga matasa su guji wannan hali na harkar daba da shaye-shaye, domin ni ma da kuka gani ina yi ba ɗan daba ba ne, faɗakarwa nake yi a game da illar shaye-shaye da kuma harkar daba ɗin. Don haka ni ba ɗan daba bane.”