Rarara, Ali Nuhu da ‘yan fim sun ba Binta Miko Yakasai tallafin gaggawa - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Rarara, Ali Nuhu da ‘yan fim sun ba Binta Miko Yakasai tallafin gaggawa

Nov 26, 2024


Rashin lafiya: Rarara, Ali Nuhu da ‘yan fim sun ba Binta Miko Yakasai tallafin gaggawa


Mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu Rarara da jarumi Ali Nuhu sun ba da tallafin gaggawa ga tsohuwar jaruma Hajiya Binta Miko Yakasai saboda rashin lafiyar da take fama da shi na ƙonewar jini.


Tun a ‘yan kwanakin baya dai ‘yan fim da suke cikin group na Kannywood Vangerd bisa jagorancin Nasiru Gwangwazo sun haɗa mata N55,000 aka kai mata domin taimakawa a game da rashin lafiyar ta ta.


A jiya Asabar ne Rarara ya bayar da tallafin N150,000 ta hannun Shugabar Kungiyar Tsofaffin Jaruman Kannywood Mata Masu Aure (KAHOWA), Hajiya Sakna Gadaz Abdullahi, yayin da Ali Nuhu, wanda shi ne Manajan Daraktan Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), ya ba da gudunmawar N100,000 a yau.


Mujallar Fim ta ruwaito cewa a kwanan baya ‘yan fim da suke cikin guruf ɗin Kannywood Vanguard a WhatsApp, bisa jagorancin Nasiru Gwangwazo, sun haɗa mata N55,000 aka kai mata domin rashin lafiyar nata.


Binta Miko Yakasai tana cikin yanayi na rashin lafiyar da har ya kai ta ga kwanciya a Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed da ke Kano, a ɓangaren bayar da agajin gaggawa.


Binta tsohuwar jaruma ce tun a farkon kafa Kannywood fim.


Ta haɗu da wannan larura ta sankarar ƙonewar jini inda ake canza mata jini a duk bayan sati biyu.


Kasancewar yanayi na rayuwa da kuma tsawon lokaci da ta samu kan ta a cikin wannan larura sun sa komai nata ya ƙare, don haka take buƙatar tallafi domin ceto rayuwar ta.


A lokacin da mujallar Fim take jin ta bakin ta a game halin da take ciki, da kuma tallafin da ta samu, Binta Miko Yakasai ta ce, “Babu abin da zan ce da ‘yan Kannywood sai dai godiya. Domin sun nuna mini halasci ba su yada ni ba. Saboda haka ina alfahari da kasancewa ta a cikin mutane masu taimako da kuma jinƙai.


“Ina godiya ga Allah. Sannan ina miƙa godiya ta ga dukkan jama’ar da suka haɗu suka ba ni tallafi.


“Na ga gudunmawa ta farko da Nasiru Gwangwazo ya haɗa dubu hamsin da biyar aka kawo mini. Sannan Dauda Kahutu Rarara shi ma ya bayar da dubu ɗari da hamsin an kawo mini. Sai kuma Ali Nuhu da shi ma ya bayar da dubu ɗari aka kawo mini.


“Dukkan gudunmawar ta zo gare ni, na karɓa. Ina yin godiya da ‘yan Kannywood ɗaiɗaiku da suka haɗa kuɗi ta wajen Nasiru Gwangwazo, da kuma Ƙungiyar Tsofaffin Jaruman Kannywood masu aure, KAHOWA, da suka yi hanyar samar mini taimako daga Dauda Kahutu Rarara da kuma Ali Nuhu.


“Allah ya saka wa kowa da alkairi. Allah ya ƙara mana arziki a masana’antar Kannywood.


“Kuma jama’a ina neman a taya ni da addu’ar Allah ya ba ni lafiya.”