Yadda Yan sanda suka cafke Jaruma Amal umar tare da karbe Motarta - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Yadda Yan sanda suka cafke Jaruma Amal umar tare da karbe Motarta

Oct 17, 2022

Jarumar Kannywood Amal Umar ta nemi Kotu ta hana mataimakin sufeton ƴan sanda mai kula da shiyya ta ɗaya da Kwamishinan ƴan sandan Kano da wani ɗan sanda mai bincike kamata.


Amal ta shigar da ƙorafinta a kotun jiha mai lamba 17 da ke Miller Road a Kano, inda ta ke neman a dakatar da ƴan sandan daga yunƙurin sake kamata.shafin freedom radio kano na ruwaito.

Rahotonni sun ce ƴan sandan sun nemi Amal ne bisa zargin damfara da ake yiwa saurayinta mai suna Ramadan.


Wani mai suna Alhaji Yusuf Adamu ne yi ƙorafi ga ƴan sandan bisa zargin Ramadan ya karɓi kuɗi har miliyan arba’in a hannunsa da zummar kasuwancin sayar da wayoyi.

Bayan da ƴan sanda suka kamar Ramadan tare da soma bincike sai ya ce, ya siyawa Amal ɗin Mota, sannan ya kama mata shago ya zuba mata kaya na miliyan biyar.


Ya ce, ya kuma bata miliyan uku domin ta biya wa mahaifinta wasu kuɗaɗe ake binsa.

Hakan ne ya sanya ƴan sanda suka cafke jaruma Amal Umar, tare da karɓe motar, sannan kuma suka ci gaba da bincikarta, abin da ya sa ta garzaya kotu.


Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, Barista Yusuf Dan Sulaiman lauyan Alhaji Yusuf Adamu ya nemi a sanya su a cikin wanda ake ƙara.

A nan mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya sanya ranar 16 ga watan Disamba mai kamawa domin duba buƙatar lauyan.


Bayan fitowa daga Kotun Freedom Radio ta so jin ta bakin lauyar Amal Umar wato Barista Adama Usman, amma ta ce ba za ce komai a lokacin.

[Via] - HLoaded