Nabar Sana’ar Fim daga yau har abada- Jaruma Maryam lawal
Wata matashiyar jaruma a masana’atar shirya fina finai ta kannywood Maryam lawal wanda ta bayyana hakan a shafin ta na sada zumunta a manhajar tiktok mai suna @maryamlawal03 inda tafi hakan a cikin wani faifan bidiyon, ta yi bidiyon a cikin nadama inda take cewa.
ATTENTION
For More Update Join Our WhatsApp Group 👇🏻
https://chat.whatsapp.com/GdEk2acGy4X8FFifk2wRtj
Follow Us On Google News 👇🏻
Join Our Twitter Group 👇🏻
https://t.me/naijastickfansgroup
“Na bar harkar fim har abada. Ina neman addu’arku da samun sana’ar da ta fi wannan da kuma miji nagari nayi aure na rayu cikin sunnar Manzon Allah Muhammad (sallallahu alaihi wasallam).
Ni na bar wannan harka ta fim, kuma ina fatar kowa ma ya bar wannan harkar har abada don ba sana’a ba ce. Ban damu da zagi ko aibantawa da wani ko wata zasu mun ba.
Ba don kowa na shiga harkar fim ba, ba kuma don wani na fita ba sai don neman rahamar Ubangiji Allah Ta’ala.
Don Allah maza da mata su taya ni da addu’ar alheri. Waɗanda ba zasu mun addu’ar alheri ba don Allah su yi shiru. Zaginsu ba zai canza mun ra’ayina na neman ceton Ubangijina ba”
Maryam lawal wanda dai yanzu ne ta ke tasowa a masana’atar wadda ba kowa ya wayeta a matsayar jaruma mai taka leda a masana’atar ba inda ta kara da cewa.
“Ba wai haka kawai nabar fim ba a’a ina da dalilai masu kwari da na tsaya nayiwa kaina karatun tanatsu da ƙiyamul laili, kuma ina fatan Allah ya ganar da duk wasu da suke ciki da ba alkhairi ba.”