Yawan Bincikar Wayoyin Mazaje ke jawo Mutuwar Aure – Mansurah Isah - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Yawan Bincikar Wayoyin Mazaje ke jawo Mutuwar Aure – Mansurah Isah

Dec 17, 2023


Yawan Bincikar Wayoyin Mazaje ke jawo Mutuwar Aure – Mansurah Isah:

Yawan mutuwar aure a wanga zamani na mu ya yi yawa, zawarunnai sun yi yawa.., tsohuwar Uwargidan Sani Danja, kamar yadda Hausaloaded suka ruwaito Mansurah Isah ta bada shawarwari yanda za’a samu mafita. Mansurah Isa, matar sanannen Jarumin shirin Kwaikwayo kuma Mawaƙin Hausa hiphop, cewa da Sani Danja, ta bayyana dalilan da ke janyo yawan mace-macen aure tsakanin maza da mata a wanga zamanin na mu. Tsohuwar Jarumar ta Kannywood ta bayyana hakan ne a hirar ta da jaridar Daily Trust, tacce so da yawa ta kan zama makamniya, bebiya, kurma dan auren ta ya yi ƙarko.

ATTENTION

For More Update Join Our WhatsApp Group 👇🏻

https://chat.whatsapp.com/GdEk2acGy4X8FFifk2wRtj

Follow Us On Google News 👇🏻

Naijastick On Google News 

Join Our Twitter Group 👇🏻

https://t.me/naijastickfansgroup

Kamar yadda Jaridar Gobirmob na ruwaito. Tsohuwar Uwargidan Sani Danja ta ce yawan duba wayoyin mazaje da mataye ke yi shi ke kawo cikas a auratayya, sanda an ka tambaye ta sirrukkan daɗewar auren su. Uwar ɗiyan Sani Danja ta ce auren ta da shi ba abu ne mai sauƙi ba.

Tacce; “Fitaccen jarumi ne ta aura, kuma baya ga haka shi kyakkyawa ne, attajiri. Wadanga matakan su ne abubuwan da ƴanmata ke son samu daga mazaje. Ƴanmata na-roƙon kula shi. I na iyakacin bakin kokari na wajen gano irin namijin da na aura. Na auri jarumi dan ni ma jaruma ce saboda masoya na iya kakaba ma ka abunda ba shi ba. Mi kubke tsammani daga namijin da addinin shi ya ma shi umarni da auren mata guda huɗu?

Daya daga abubuwan da sun ka sa auren mu ya dore shi ne rashin bincikar wayarnshi da ba ni yi tsawon rayuwar auren mu. Kun san, matsalar mata na bincikar wayoyin mazajen su shi ne jigo wajen jawo mutuwar auren su. Idan macce ta binciki wayar mijin ta ta gano abunda bai kamata ta gani ba, zai tada ma ta hankali, wani sa’in harda auren ta.

Amman idan ta yi nesa da wayar mijin ta, na’urar laptop ɗin shi da sauran abubuwa na shi na kai, za ta yi rayuwar auren ta cikin kwanciyar hankali. I na tsammanin wanga shi;ne sirrin da ya sa auren mu ya dore har tsawon lokaci.”