Lauyoyin Murja kunya Sun Yi Barazanar Maka Gwamnatin Kano A Kotu
Lauyoyin da ke kare fitacciyar jarumar TikTok din nan, Murja Ibrahim Kunya, sun ba Gwamnatin Jihar Kano wa’adin awanni 24 da ta ba su izinin ganinta ko kuma su maka ta a gaban kuliya.
Hakan na kunshe ne cikin wata takarda da lauyoyin Murja — Aliyu Usman Hajji da Saddam Sulaiman — suka fitar suna kalubalantar matakin ci gaba da hana su ganin wadda suke karewa.
Wadanda lauyoyin suka zarga da hana su ganin Murjar sun haɗa da Asibitin Muhammad Abdullahi Wase da ke karkashin kulawar Hukumar Asibitocin Jihar Kano da Hukumar Hisbah ta jihar da Magatakardan Kotun Shari’ar Musulunci ta Kwana Hudu PRP.
Aminiya ta ruwaito cewa, Mai Shari’a Nura ne Yusuf ya ba da umarnin a yi wa Murja gwajin kwakwalwa a Asibitin Gwamnatin domin tabbatar da lafiyar kwakwalwarta.
Alkalin ya ba da umarnin ne bisa zargin ba ta cikin hayyacinta a lokacin zaman kotun na farko da aka gurfanar da ’yar TikTok din.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce ta soma gurfanar da Murja kan zargin tayar da hankalin jama’a, bata tarbiyya da kuma koyar da karuwanci.
A cewar lauyoyin Murja, “bisa bincikenmu wacce muke karewa ta yi biyayya ga umarnin kotu inda a halin yanzu tana Asibitin Kwararru na Muhammad Abdullahi Wase (Asibitin Nassarawa) karkashin kulawarku.”
Lauyoyin sun kara da cewa, “sai dai a ranar 22 ga watan Fabarairun mun nemi ganin ta don tattaunawa da ita, amma an hana mu ganin ta wanda hakan ya ci karo da Kundin Tsarin Mulkin Kasa na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
A matsayinmu na lauyoyi mun sani cewa kowane mutum yana da ’yancin ganin lauyansa musamman a lokacin da ake tuhumarsa da aikata laifi kamar yadda take kasancewa da Murja a yanzu.
“Don haka daga wannan lokaci mun ba Asibitin wa’adin awanni 24 da su yi gaggawar janye matakin da suka ɗauka na hana mu ganin ta domin hakan keta haƙƙin biladama ne.”
A wata takarda da Aminiya ta sami kwafin ta gano cewa takardar gargadin ta isa ga Asibitin Kwararru na Muhammad Abdullahi Wase da kuma Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, inda wasu jami’an hukumomin biyu suka rattaba hannu akan takardar da ke nuni da cewa sun karɓi takardar a hannunsu.
-Aminiya Hausa